Yadda Real Madrid ta kai wasan karshe

Real Madrid 2-2 Bayern Munich (4-3)

Anan muka kawo karshe wannan sharhi da muke kawo muku.

Sai ku kasance da mu a gobe Laraba inda AS Roma za ta karbi bakuncin Liverpool.

Ka da a manta Liverpool ta lashe wasan farko da ci 5-2.

Muna taya Real Madrid da magoya bayanta murna

Bayern ta ji zafin wasan

Real Madrid 2-2 Bayern Munich (4-3)

Yan wasan Bayern na ta faduwa a kasa, wasunsu na kuka.

Hakika sun ji zafin wannan wasan, musamman ganin yadda Real ta saba doke su a irin wannan matakin.

Navas ya cece Madrid

Real Madrid 2-2 Bayern Munich (4-3)

Sau takwas golan Real Madrid Keylor Navas na kade kwallo a dare yau.

Wannan shi ne adadi mafi yawa da wani golanta ya taba yi a wasan kifa-daya-kwale na gasar.

Za a iya cewa shi ne ran Madrid a wannan wasa.

Getty Images

Advertise with Hausa NG
zumam :